Wata cibiyar bincike a nan kasar Sin ta bayyana cewa lokacin hutu na mako daya a kasar don murnar shiga sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar zai kara tafiye tafiyen da jama'a ke yi zuwa wuraren da ke jawo hankalin jama'a, kana zirga-zirgar da za a yi zuwa wuraren yawon shakatawa a kasar za su kai kusan miliyan 250, kuma kudin shiga a wannan bangaren zai karu da kusan kashi 13 a cikin 100 wato renmimbi na Sin biliyan 140 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 22.84.
Kamar yadda alkalumma na cibiyar yawon shakatawa ta Sin ta nuna za a samu karuwar harkokin tafiye tafiye a cikin gida a wannan shekarar sannan za a samu karin masu zuwa kasashen waje, inda kasashe kamar su Thailand, Korea ta kudu, Japan da Amurka za su zama a kan gaba wanda Sinawa masu yawon shakatawa zasu ziyarta.