Hukumar kula da masu yawon shakatawar NTA ta kasar Sin ta bukaci rassan hukumomi na garuruwa da su karfafa matakan tsaro, inganta shirin ko ta kwana, daukan matakai wajen tafiyar da karuwar baki a wuraren da ake sha'ani.
Haka kuma ta bukaci duk wuraren da ake wani sha'ani da cibiyoyin kula da tafiye tafiyen su rika ba da bayanai a kan lokaci ga baki masu ziyara.
A karkashin dokar yawon shakatawa na kasar Sin, wuraren da ake taro ya kamata su bayar da cikakken bayani ga baki kuma sun ba da rahoto ga karamar hukumar da suke karkashin shi idan har yawan masu yawon shakatawar zai wuce adadin da ake tsammani, saboda a san matakin da za'a dauka domin rage yawan bakin da kuma samar da tsaro. Sinawa suna yin kwanaki uku na murnar sabuwar shekara. (Fatimah Jibril)