Sinawa sun kwashe fiye da kashi 55 cikin 100 na masu balaguro bisa zirga zirgar jiragen sama tsakanin Sin da Amurka tun lokacin da kamfanonin jiragen saman kasar Sin suka fara amfani da hanyoyin jiragen sama tare da manyan jiragen sama, musammun jiragen sama samfurin Boeing 747 da 777 da kuma jiragen sama samfurin Airbus A380, in ji mista Wang.
A cewar hasashen kungiyar kasa da kasa kan sufurin jiragen sama, yawan adadin masu balaguro ta jiragen saman cikin gida a kasar Sin zai karu da kashi 10.8 cikin 100 a shekarar 2015, a yayin da adadin karuwar zirga zirga jiragen sama tsakanin Sin da Amurka, Sin da Turai da kuma Sin da Asiya da Pasifik zai cimma a jere kashi 10 cikin 100, kashi 9 cikin 100 da kashi 4 cikin 100.
Bayan haka, wata dama mai kyau shi ne kamfanonin jiragen saman kasar Sin, za su kaddamar da zirga zirgar jiragen sama tun daga birane mafi kankanta, kana kuma kamfanonin jiragen sama masu arha na jama'a za su shiga kasuwar zirga zirgar jiragen sama na jama'a ta kasar Sin. (Maman Ada)