in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kasa da kasa sun mika sakon murnar sabuwar shekara ga kasar Sin
2015-02-19 16:50:44 cri

Babban magatakardan MDD Mr Ban Ki-Moon, ya bayyana fatan alherin sa ga dukkanin Sinawa dake fadin duniya, tare da taya su murnar shiga sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin.

Cikin wani sakon bidiyo da ya gabatar a jiya Laraba, Mr Ban ya yi amfani da harshen Sinanci wajen bayyana kalmar "barka da sabuwar shekara" kafin daga bisana ya bayyana kyakkyawan fatan sa ga al'ummar kasar ta Sin, game da shiga sabuwar shekarar, tare da godiya ga irin goyon bayan da Sinawa ke baiwa MDD.

Kaza lika Mr. Ban ya jinjinawa gudunmawar da Sinawa ke bayar wajen sa kaimi ga kokarin da majalisar ke yi na wanzar da zaman lafiya, da samun bunkasuwa, tare da tabbatar da hakkin Bil Adam.

A cikin jawabinsa, Mr Ban ya ce, wannan shekara ce ta cika shekaru 70 da kafuwar majalisar, kuma shekarar rago ce a kasar Sin. Bisa al'adun Sinawa, rago na alamanta kwanciyar hankali da tausayi. Don haka ya yi kira da a yi amfani da babbar ma'anar wannan shekara, domin tausayawa, da ba da kulawa yayin da ake kokarin tabbatar da manyan muradun majalisar.

A karshe ya yi fatan samun lafiyar jiki, da haduwar iyalai, tare da samun babban ci gaba cikin sabuwar shekarar ta rago.

A wani ci gaban kuma, shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, shi ma ya gabatar da jawabin nuna kyakkyawan fata game da shiga sabuwar shekarar Sinawa, tare da fatan alheri ga dukkan Sinawa baki daya.

Dadin dadawa, shugaban kasar Faransa François Hollande, da firaministan kasar Birtaniya David Cameron‎ da dai sauran shugabannin kasa da kasa, su ma sun gabatar da sakwanninsu na fatan alheri game da shiga sabuwar shekarar ta Sinawa. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China