in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Faraministan Mali ya kafa gwamnatinsa mai kunshe da mambobi 34
2013-09-09 10:52:17 cri

Sabon faraminstan kasar Mali, Oumar Tatam Ly, ya kafa gwamnatinsa mai kunshe da mambobi talatin da hudu a ranar Lahadi, a wani labarin kafar talabajin din kasar ORTM. Bayan an nada shi faraministan kasar Mali a ranar Alhamis da ta gabata wato kwana daya bayan bikin rantsar da sabon shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita, mista Ly ya nada mutane talatin da hudu wadanda a cikinsu akwai mace hudu domin kafa gwamnatinsa. Shugaba Ibrahim Boubacar Keita ya nada ministocin bisa ra'ayin faraminista. A cikin wadannan mambobin gwamnatin mista Ly, akwai wasu daga cikin tsohuwar gwamnatin wucin gadi dake karkashin mista Diango Cissoko.

Haka kuma shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita da aka fi sani lakabin IBK ya kirkiro da kujerar ministan sasanta 'yan kasa da kula da cigaban yankunan arewacin kasar a cikin wannan gwamnatin farko dake karkashin shugabancinsa da aka nada mambobinta a ranar Lahadi. Ma'aikatar da aka baiwa nauyin sasanta 'yan kasa da kula da cigaban arewacin kasar Mali, an mika ta ga hannun mista Cheick Oumar Diarra. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China