in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kafa sabuwar gwamnati a kasar Senegal
2013-09-03 10:35:58 cri

Wata sanarwa da mahukuntan kasar Senegal suka bayar ta bayyana cewa, a ranar Litinin ne firaministar kasar Aminata Toure ta kafa sabuwar gwamnati a kasar da ke yammacin Afirka bayan nada ta bisa wannan mukami a kwanakin baya.

Youssou Ndour, tsohon minista a gwamnatin da ta gabata ba ya cikin jerin sabbin ministocin gwamnati guda 32 da aka nada. Shi dai mawakin wanda ya shiga harkokin siyasa, an rantsar da shi mukamin minista ne a watan Afrilun shekarar 2012, bayan da aka hana shi tsayawa takarar zaben shugaban kasa a watan Afrilu din shekarar 2012.

Sidiki Kaba shi ne ya maye gurbin mukamin madam Toure na ministan shari'a a sabuwar gwamnatin. A ranar Lahadi ne dai madam Toure mai shekaru 51 ta zama mace ta biyu 'yar kasar Senegal da aka nada a matsayin shugabar gwamnati tun lokacin da kasar ta samu 'yancin kanta a shekarar 1960, yayin da madam Mame Madio Boye ta kasance mace ta farko a kasar da ta shugabancin gwamnatin kasar daga watan Maris na shekarar 2011 zuwa watan Nuwamban shekarar 2012.

Kafin nadin nata, Madam Toure, sai da shugaban kasar ta Senergal Macky Sall ya tsige tsohon firaministan kasar Abdoul Mbaye, wanda ya rike mukamin shugaban gwamnati bayan da Sall ya lashe zabe a watan Maris na shekarar 2012. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China