in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kasar Sin sun gana da jakadun kasashen waje
2013-04-03 21:26:44 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, Firaminista Li Keqiang da Mataimakin Shugaban Kasar Li Yuanchao a yau Laraba 3 ga wata suka gana da jakadun kasashen waje da kuma wakilan manyan kungiyoyin kasa da kasa dake nan birnin Beijing, fadar gwamnatin kasar, wadanda yawansu ya kai180.

A lokacin wannan ganawar dai da aka yi a babban zauren jama'ar kasar, shugabannin na Sin sun bukaci jakadun da kuma wakilan kungiyoyin kasa da kasa da su isar da sakon fatan alheri ga nasu shugabannin kasashen tare da mika cikakkiyar godiyarsu bisa ga taimakon da suke ba su wajen inganta zumunci da hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da nasu kasashen.

Shugabannin na Sin sun jaddada kudurin kasar na ganin ta bi hanyar samar da zaman lafiya da cigaba tare da bayyana dabarunta a fili na hanyoyin da za ta bi domin moriyar juna da samun nasara tare.

Haka kuma shugabannin sun yi alkawarin bin tsarin samar da zaman lafiya da cigaba, sannan kuma za su inganta yanayin abota mai haske da zai karfafa dankon zumunci tsakanin kasar da sauran kasashen da ma kungiyoyi na duniya.

A nasu bangaren jakadun na kasashen wajen da wadannan wakilan kungiyoyin sun gabatar da sakon fatan alheri da gaisuwa daga nasu shugabannin zuwa ga shugabannin kasar Sin da ma al'ummar Sinawa baki daya. Sannan suka nuna imaninsu na ganin cewa, raya hulda da kasar Sin wani babban alfanu ne, don haka suka yi alkawarin yin duk abin da ya kamata don ganin hakan ya cigaba da wanzuwa a tsakanin kasashensu da kasar ta Sin.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China