in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar da shugabannin kasar Sin suka kai a kasashen waje ta sheda manufar kasar a fannin diplomasiyya
2013-05-31 20:28:19 cri
Kamfanin dillancin labaru na kasar Sin Xin Hua ya rubuta wani sharhi mai taken 'Ziyarar da shugabannin kasar Sin suka kai a kasashen waje ta sheda manufar kasar a fannin diplomasiyya', inda aka yi nuni da cewa, cikin watanni 2 na bayan nan da sabbin shugabannin kasar Sin suka hau karagar mulki, sun kai ziyara a kasashe da yawa, wadda ta shafi kusan dukkan nahiyoyin duniya. Wannan batu, a ganin wasu masana, ya sheda tsarin da kasar Sin ke bi wajen hulda da kasashen waje, inda ta mai da hankali kan wasu abubuwa masu muhimmanci, tare da kokarin kiyaye daidaituwa.

Dangane da batun, Shen Jiru, wani masanin kasar Sin mai binciken tattalin arziki da siyasar duniya, ya ce yadda shugabannin kasar Sin suka zabi kasashen da suka kai ma ziyara ya dace da manufar diplomasiyyar kasar cewar 'mai da hankali kan manyan kasashe da kasashe makwabta, da dogaro kan raya hulda tare da kasashe masu tasowa, gami da wani tsarin da ya kunshi sassan duniya daban daban', wadda kuma ta bayyana ra'ayin gwamnatin tsakiyar kasar Sin na neman raya hulda da kasashe daban daban.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China