Bayan da aka gudanar da zaben 'yan majalisun kasar Djibouti a ranar 22 ga watan Febrairun da ya gabata, an kafa sabuwar majalisar dokoki a kasar, daga baya, shugaban kasar Ismail Omar Guelleh ya kafa sabuwar gwamnatin kasar a ranar Lahadin da ta gabata.
Al'ummar kasar Djibouti ta yi jiran ganin kafa wannan sabuwar gwamnati tun bayan ficewar Dileita Mohamed Dileita daga mukamin faraministan wannan karamar kasa dake kusurwar nahiyar Afrika tun shekaru goma sha uku da suka gabata.
Aka baiwa mista Abdoulkader Kamil Mohamed dake rike da kujerar ministan tsaron kasar har zuwa wannan lokaci mukamin firaminista. Sabuwar gwamnatin kasar na kunshe da ministoci 17, karamin ministan 2 da kuma sakataren kasa 3. Ministoci biyar sun shigo a yayin da ministoci 7 suka cigaba da rike mukamansu, ko aka canja masu kujera. (Maman Ada)