in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nigeria za ta bullo da aiki da na'ura wajen taimaka ma baki shigowar kasar
2013-06-19 10:32:38 cri

Gwamnatin tarayyar Nigeria a jiya Talata 18 ga wata, ta sanar da cewa, za ta bullo da wata sabuwar hanyar amfani da na'urar da za ta taimaka a rage cunkuso da bata lokaci wajen ayyukan da suka shafi shigowar baki a kasar.

Ministan al'amuran cikin gida Abba Moro wanda ya sanar da hakan a wajen ganawa da manema labarai na duk wata da ma'aikatu daban daban su kan yi a Abuja, ya ce, bullo da wannan sabuwar na'ura tuni majalissar zartarwa ta riga ta amince da shi.

Ya yi bayanin cewa, makasudin bullo da wannan na'urar shi ne domin cire duk wani cikas da a kan gamu da shi wajen samar da takardun izinin shigowar kasar don zama da kuma na zuwa domin kasuwanci.

Shi dai wannan na'urar, in ji shi, yana saka duk ayyukan da ya jibanci hakan ya yi sauri kuma a kammala shi a cikin lokaci saboda ba za'a yi amfani da takarda ba kamar a baya.

Haka kuma wannan sabon salo zai hana bukatar sai mai neman takardan ya zo da kansa tun da zai iya ba da amsar da ake bukata ta na'urar, don haka, ba lallai sai ma'aikatan ofishin kula da hakan sun gan su ba, sannan kuma wannan zai rage zargin cin zarafi da ke yi ma baki.

Abba Moro ya ce, shugaban kasar Nigeria Goodluck Jonathan ya kuma amince da ba da takardun izinin shiga kasar ga wassu kamfanoni da manyan jami'an cibiyoyin da aka tantance su nan take idan har suka bukaci shiga kasar daga ko'ina.

Ya kara da cewa, wannan sabuwar takardar izinin shiga zai kuma gaggauta cigaban tattalin arziki domin zai samar da ayyukan yi da kuma inganta yawon shakatawa, sannan kuma 'yan kasashen da yanzu haka suke da yarjejeniyar ba da takardun izinin shiga kasar a tsakaninsu, su ma za'a ba su takardan izinin shiga nan take. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China