A yayin ganawar, Li Keqiang ya bayyana cewa, cutar Ebola tana daya daga cikin manyan kalubalen da kasashen duniya suke fuskanta tun a shekarar bara. Jama'ar kasar Sin sun bada gudummawa cikin gaggawa ga al'ummar kasashen da ke fama da cutar Ebola, da shirya manyan ayyukan bada taimako a fannin kiwon lafiya, baya ga kudade da kayayyaki da aka ba da a lokuta daban-daban, da tura likitoci da masanan kiwon lafiya fiye da dari daya zuwa kasashen don horar da ma'aikatan jiyya dake wurin.
A nata jawabin, Dr. Margaret Chan ta nuna yabo ga kasar Sin kan muhimmiyar rawa da ta taka wajen yaki da cutar Ebola da samar da gudummawa da nuna goyon baya ga kasashen da ke fama da cutar. Ta bayyana cewa, ana ci gaba da fuskantar kalubale kan yaki da cutar Ebola, don haka ana bukatar kasashen duniya da kasashen da ke fama da cutar da su yi kokari tare wajen tinkarar cutar. Ayyukan da kasar Sin ta gudanar da farko sun zama abin koyi ga sauran kasashen duniya, ta yadda za su taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga yaki da cutar. Hukumar WHO tana son kara yin hadin gwiwa tare da kasar Sin don ci gaba da sa kaimi ga kasa da kasa da su yi kokari tare ta yadda a karshe za a yi nasarar yakar cutar . (Zainab)