in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin zai halarci taron Davos na 2015
2015-01-19 09:38:18 cri

Jakadan kasar Sin dake ofishin MDD a kasar Geneva Wu Hailong ya ce, halartar dandalin tattaunar tattalin arziki na duniya (WEF) da firaministan kasar Sin Li Keqiang zai yi zai kara tabbacin da duniya ke da shi kan tattalin arzkin kasar Sin.

Wu Hailong wanda ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua ya ce, kasar Sin na dora matukar muhimmanci ga taron da ke gudana a kowa ce shekara.

A yayin taron, firaminista Li zai kuma bayyana manufofin Sin na cikin gida da ketare, sannan zai mayar da martabi game da damuwar da sauran kasashen duniya ke yi kan kasar Sin, kara tabbacin kasashen duniya game da makomar tattalin arzikin kasar Sin.

Bugu da kari Li Keqiang zai yi musayar ra'ayoyi da mahalarta taron kan yanayin na duniya, da yadda tattalin arzikin duniya ke ciki da kuma hanyoyin magance wadannan kalubale.

Sama da mahalarta 2,500 daga sama da kasashe 140 da ke wakiltar gwamnatoci da hukumomin kasa da kasa, 'yan kasuwa da masana, kungiyoyin fararen hula da kafofin watsa labarai ne za su halarci taron na wannan shekara.

Za a gudanar da taron ne daga ranar 21 zuwa 24 ga wannan wata a birnin Davos na kasar Switzerland, inda ake sa ran bullo da matakan magance manyan kalubalen da duniya ke funkanta. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China