in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya isa kasar Switzerland don halartar taron shekara-shekara na dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya na shekarar 2015
2015-01-21 10:21:37 cri
Bisa gayyatar da shugaban kwamitin dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya Klaus Schwab da gwamnatin kasar Switzerland suka yi masa, a jiya da yamma ne firaministan kasar Sin Li Keqiang ya isa kasar Switzerland don halartar taron shekara-shekara na dandalin tattaunawar da zai gudana a birnin Davos da kuma kai ziyarar aiki a kasar Switzerland.

Li Keqiang ya bayyana cewa, yana fatan yin musayar ra'ayoyi tare da wakilai daga bangarori daban daban da ke halartar taron, kan halin da ake ciki a yankunan duniya, bude kofa da yin kwaskwarima da bunkasuwar tattalin arziki da kasar Sin take yi, da kuma batutuwan da bangarori daban daban suke maida hankali kansu a yayin taron, kana yana son yin kokari don tabbatar da zaman lafiya da na karko, da sa kaimi ga bunkasa tattalin arziki mai dorewa da daidaito a duniya.

Hakazalika kuma, Li Keqiang ya bayyana cewa, yana fatan yin musayar ra'ayoyi tare da shugabannin kasar Switzerland kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da batutuwan da suke sa lura, kana batun fannin hada-hadar kudi zai kasance sabon abin da zai sa kaimi ga hadin gwiwarsu.

A yayin taron dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya da Li Keqiang zai halarta zai kuma gabatar da wani jawabi na musamman, da yin mu'amala tare da wakilan majalisar harkokin masana'antu da ciniki ta duniya, ganawa da shugaban kwamitin dandalin tattaunawar Schwab, da kuma wasu shugabannin kasashen duniya da ke halartar taron. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China