Wani kwararre a fannin ilimin kimiyya ya ja hankulan kasashen Afirka, game da irin darussan da ya dace su koya daga yaduwar cutar Ebola, cutar da ta hallaka dubban al'ummar yammacin nahiyar.
Wata mujallar kimiyya ta birnin Nairobin kasar Kenya ce ta rawaito farfesa Vincent Pryde Kehdingha Titanji, na cewa, manyan darussan da ya dace a lura da su, sun hada da batun tasirin ilimin kimiyya wajen shawo kan cututtuka masu saurin yaduwa, da batun daukar matakai a kan lokaci, tare da tsara ayyukan shawo kan cututtuka yadda ya kamata.
Farfesa Titanji ya ce, wayar da kawunan jama'a, da ilmantar da su al'amuran da suka shafi kiwon lafiya, tare da samar da muhimman kayayyakin da ake bukata don kare yaduwar cututtuka, na da ma'anar gaske a wannan fanni.
Kaza lika ya jaddada muhimmancin shigar da shuwagabanni a matakin farko, da al'ummun dake fama da yaduwar cutuka, cikin shirin magance cututtuka a dukkanin matakai.
Titanji ya kuma jinjinawa manyan kasashen duniya, musamman ma kasashen Sin, da Amurka da Birtaniya da Faransa, bisa irin tallafin da suke bayarwa a yakin da ake yi da cutar Ebola, yana mai cewa, managartan matakan da ake dauka, na da matukar tasiri wajen cimma nasarar da aka sanya gaba. (Saminu)