in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya halarci taron wakilan majalisar 'yan kasuwa da masana'antu na taron Davos
2015-01-22 10:48:47 cri
A jiya da yamma ne firaministan kasar Sin Li Keqiang ya halarci taron tattaunawa tare da wakilan majalisar 'yan kasuwa da masana'antu na dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya a birnin Davos.

Game da shirin yin kwaskwarima da kasar Sin ke aiwatarwa, Li Keqiang ya bayyana cewa, a shekarar 2015, kasar Sin za ta ci gaba da sa kaimi kan yin kwaskwarima a manyan fannoni, inda za ta mayar da hankali wajen daidaita dangantakar dake tsakanin gwamnati da 'yan kasuwa.

Bugu da kari Sin za ta kara yin kwaskwarima kan tsarin yin binciken ayyukan gwamnati, wannan zai taimaka wajen inganta harkokin kasuwanci da samar da yanayi mai adalci a kasuwa. Kana za a kara yin kwaskwarima a fannonin haraji da hada-hadar kudi, da gabatar da kasafin kudi a fili, da kara zuba jari ga ayyukan da za su shafi al'ummar kasar.

Game da manufofin tinkarar sauyin yanayi da kasar Sin take gudanarwa, Li Keqiang ya bayyana cewa, Sin za ta yi kokari wajen rage yawan makamashin kwal da ta ke yin amfani da shi cikin sauran makamashi, da sa kaimi ga yin amfani da fasahohin tsabtace kwal a nan gaba. A matsayinta na babbar kasa mai tasowa, kasar Sin za ta yi kokarin tinkarar sauyin yanayi, da kiyaye muhalli, da kuma daukar alhaki tare amma da bambanci.

Game da shigar kasar Sin kasuwar hada-hadar kudi ta duniya, Li Keqiang ya bayyana cewa, kasar Sin tana kokarin ganin ana amfani da kudin kasar na RMB a tsakanin kasa da kasa da zuba jari da gudanar da harkokin kudin Sin a kasashen waje, wannan na taimaka wajen ci gaban kasar Sin, da sanya kasar ta Sin dacewa da tsarin hada-hadar kudi na duniya, da bunkasuwar kasuwanni, kana zai b ada gudummawa wajen tabbatar da tsarin hada-hadar kudi na duniya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China