Zagaye na biyu na kamfen kawar da cutar Ebola a yankin yammacin kasar Saliyo ya fara a ranar Litinin da zummar rage yawan masu kamu da cutar Ebola a yankin Freetown, babban birnin kasar da kuma kewayensa. Darekta janar na cibiyar kasa kan yaki da Ebola (NERC), Palo Conteh ya bayyana cewa, manufar wannan zagaye na biyu shi ne na dakatar da yaduwar wannan cuta, da kuma kara cimma nasarori bisa wadanda aka samu a zagayen farko, daga ranar 17 ga watan Disamban shekarar 2014 zuwa 15 ga watan Janairun shekarar 2015.
Mista Conteh ya shaida wa manema labarai a ranar Litinin cewa, gaba daya matsalar a shiyyar ta kyautatu fiye da yadda ake tsammani, amma wannan ba ya nufin ba za mu ci gaba da aikin kawar da cutar ba, domin har yanzu akwai wuraren dake bukatar sa ido da kulawa. A yayin zagayen farko na kamfen a cikin watan Disamban shekarar da ta gabata, an samu kididdiga, tare da kwantar masu fama da rashin lafiya kimanin 9334, tare da gano 263 daga cikinsu dake dauke da cutar Ebola, kuma aka tura su asibitocin musamman domin samun jinya.
An yi mana manyan alluna dauke da bayanai game da cutar Ebola kan hanyoyi a ranar Litinin da safe a muhimman wuraren birnin, a yayin da kuma tawagogin ma'aikatan lafiya suna bin gida gida domin isar da sakon fadakarwa ga jama'a. Kuma kimanin ma'aikatan lafiya 20.000 ke halartar wannan kamfe. (Maman Ada)