in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya gana da shugaban taron Davos
2015-01-21 10:31:36 cri

A jiya Talata 20 ga wata da dare ne, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da shugaban taron dandalin tattaunawar tattalin arzikin kasa da kasa Klaus Schwab a birnin Davos na kasar Switzerland.

A yayin ganawarsu, Li Keqiang ya bayyana cewa, taron Davos na da tasiri mai muhimmanci ga tattalin arzikin duniya. Kana tattalin arzikin kasar Sin na ci gaba da karuwa cikin yanayi mai kyau, duk da wasu canje-canje da tattalin arzikin kasar Sin da na kasashen ketare ke fuskanta. A nan gaba, kasar Sin za ta ci gaba da gudanar da harkokin kudi yadda ya kamata, domin tabbatar da bunkasuwar aikin cikin yanayi mai kyau da karko, kana, tsarin tattalin arzikin kasar Sin na ci gaba da samun kyautatuwa a halin yanzu.

A nasa bangaren, shugaban taron Davos, Klaus Schwab ya nuna maraba ga halartar firaminista Li Keqiang a taron na Davos na shekarar bana, inda ake sa ran Li Keqiang zai yi jawabi yayin bude taron, domin gabatar da karin fasahohin kasar Sin ga samun bunkasuwar tattalin arzikin duniya. Bugu da kari, ya ce, matsayin kasar Sin cikin harkokin siyasa da tattalin arzikin kasa da kasa na ci gaba da daguwa, taron dandalin tattalin arzikin kasa da kasa na son yin hadin gwiwa tare da kasar Sin, da kuma nuna goyon baya ga kasar, ta yadda kasar ta Sin za ta iya ba da karin gudummawa cikin harkokin kasa da kasa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China