Da farko, za a kara yin gyare-gyare kan nauyin da ake dorewa hukumomin gwamnati, wato za a kara sake wa wasu gwamnati mara, sannan za a karfafa yin gyare-gyare kan manufofin biyan haraji da manufofiin ware da amfani da kasafin kudi, ta yadda za a iya yin amfani da kudaden jama'a kamar yadda ya kamata, in ji Li Keqiang.
Sannan, za a kara yin kokarin kawar da wasu shingen da ke kawo tarnaki ga kokarin kara samar da ayyukan more al'umma, ta yadda za a iya biyan bukatun da ake da su.
Bugu da kari, Li Keqiang ya ce, za a ci gaba da yin kokarin amfani da karin kasafin kudi da sauran kudaden da aka adana wajen tallafawa masana'antun da suke samar da kayayyaki da sabbin masana'antu da sauran kamfanonin da suke da nasaba da aikin gona da manoma da kauyuka da kananan masana'antu da kamfanonin ba da hidima.
Dadin dadawa, Li Keqiang ya ce, kasar Sin tana da imani da karfi, har ma tana da sharadin kawar da matsalolin da suke kasancewa a gabanta domin cimma burin bunkasa tattalin arziki da zaman al'umma kamar yadda aka tsara a shekarar bana. (Sanusi Chen)