in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arzikin Sin na tafiya kamar yadda ya kamata
2014-09-09 20:28:54 cri
Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana a ranar Talata cewa, tattalin arzikin kasar Sin na tafiya a mizanin da ya dace.

Mr. Li ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi ga masu masana'antu gabanin taron dandalin Davos na lokacin sanyi da za a yi a birnin Tianjin da ke nan kasar Sin.

Ya ce, yanzu haka tattalin arzkin Sin ya karu da kashi 7.4 cikin 100, baya ga guraben aikin yi masu kyau da aka samar, da kuma farashin kaya na kashi 2.3 cikin 100 a farkon rabin shekara, wannan na nuna cewa, al'amura na tafiya kamar yadda ake fata duk da wasu 'yan tangarda da alkaluman tattalin arzkin kasar ya fuskanta.

Ya ce, sanin kowa ne cewa, tattalin arzikin duniya na fuskantar matsalar farfadowa, don haka tattalin arzkin Sin ma ba zai tsira daga wasu matsaloli ba.

Mr Li ya ce, gwamnatin za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace don ganin an aiwatar da manufofin da aka tsara game da dorewar bunkasar tattalin arzikin kasar.

Ya kuma bayyana kudurin Sin na ci gaba da bin manufofin cinikayya cikin hadin gwiwa tare da mutunta dokokin da abin ya shafa. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China