Yayin ganawarsu, Mr. Li ya bayyana cewa, kasar Sin tana goyon bayan kokarin da kasar Mali ke yi na neman sulhunta kabilun kasar, da kuma bunkasa tattalin arzikinta, kuma kasar Sin tana son ci gaba da taimaka wa kasar Mali wajen ganin an samar da zaman lafiya a kasar, don habaka dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi.
Mr. Li ya kuma bayyana cewa, kasashen Sin da Afirka abokan arzikin juna ne, shi ya sa, daga lokacin da Sin ta sami labaran cewa, wasu kasashen yammacin Afirka na fama da cutar Ebola, nan da nan kasar Sin ta samar musu taimakon kayayyakin agaji da na hana yaduwar cutar Ebola, kana ta aike da wasu likitoci zuwa kasashen. Kasar Sin tana son yin hadin gwiwa tare da kasashen yammacin Afirka kan yaki da cutar ta Ebola, haka kuma, za ta ba da gudumawa don samar da kayayyakin kiwon lafiya da jama'arsu
A nasa bangare kuma, Shugaba Keita ya ce, kasar Sin aminiya ce ta kasar Mali da kuma dukkanin kasashen Afirka, kasarsa na matukar godiya dangane da goyon baya da taimakon da kasar Sin ta samar mata da ma sauran kasashen nahiyar Afirka wajen samun dauwamammen ci gaban zaman lafiya da kuma yaki da cutar Ebola, kasar Mali tana son yin hadin gwiwa da kasar Sin yadda ya kamata don ciyar da dangantakar zumunci dake tsakanin kasashen biyu gaba. (Maryam)