in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dandalin tattalin arziki na Davos ya lalubo bakin zaren samun karuwar tattalin arziki
2014-01-26 11:27:56 cri

A ranar 25 ga wata da dare, an kammala taron tattaunawar tattalin arziki na shekara-shekara na duniya wato Davos a hukunce. A cikin taron da aka shafe kwanaki 4 ana yinsa, mahalartar taron sun tattauna yanayin da tattalin arzikin duniya ke ciki, da kalubalen da ake fuskanta, kuma sun tattauna matakan da za a dauka don warware rikicin, da lalubo bakin zaren samun karuwar tattalin arziki.

Shugaban bankin duniya Kim Yong, da babbar jami'ar zartaswa ta asusun ba da lamuni na duniya Christian Lagarde da shugaban babban bankin Turai Mario Draghi da sauran kwararru a fannin tattalin arziki suna ganin cewa, yanzu, tattalin arzikin duniya ya kama hanyar samun farfadowa, amma ana ci gaba da fuskantar kalubale da hadarurruka sosai, ciki har da yin gyare-gyare game da tattalin arziki a kasar Sin, kuma mahalartar taron sun yi kwarin gwiwa sosai game da makomar samun karuwar tattalin arziki a kasar Sin.

A ranar 22 ga wata, an kaddamar da taron tattaunawar tattalin arziki na shekara-shekara na bana, bisa taken taron "sake sabunta tsarin kasa da kasa da kuma irin tasirin da zai kawo harkokin siyasa, kasuwanci da zamantakewar al'umma" inda aka samu halartar 'yan siyasa da 'yan kasuwa da kwararru sama da 2500 da suka fito daga kasashe da yankuna sama da 100 a duniya. A watan Satumba na bana, za a yi taron shekara-shekara na taron Davos na lokacin sanyi a birnin Tianjin dake kasar Sin.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China