Wani masani dan kasar Sin Lu Ruian a cibiyar nazarin tattalin arzikin kasashen duniya Peterson ta kasar Amurka, ya bayyana cewa, sabbin shugabanni sun samu babban ci gaba wajen kyautata zaton jama'a game da tattalin arzikin kasar Sin. Kuma sun nuna wa kasashen duniya cewa Sin ta gamsu da yawan karuwar tattalin arzikinta da ya kai kashi 7 zuwa 8 cikin 100, tare da daukar wassu matakai don tabbatar da wannan karuwa.
Malami a kwalejin nazarin huldar kasa da kasa da diplomasiyya na jami'ar Nairobi dake kasar Kenya, Mumini ya ce, jawabin Mr Li ya nuna cewa, babbar gamayyar tattalin arziki ta Sin na da kwarewar daidaita bunkasuwar tattalin arziki ta duniya. Ya kara da cewa, firaministan Li ya ambaci aikin yaki da ra'ayin kare cinikin kasashensu, kuma kasashen Afrika suna fatan kasar Sin za ta ci gaba da daukar irin wadannan manufofin tattalin arziki, don ci gaba da yin mu'amalar ciniki da kasashen Afrika.(Bako)