in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shawarwarin sauyin yanayi wani muhimmin aiki ne mai nauyi na dogon lokaci, in ji Sin
2014-12-15 20:08:07 cri
A jiya Lahadi 14 ga wata ne, aka rufe taron MDD kan sauyin yanayi da aka yi a birnin Lima na kasar Peru, inda wakilan kasashen dake halartar taron suka kasa cimma wata matsaya kan wasu muhimman batutuwa game da sabuwar yarjejeniyar da ake fatan cimmawa a taron sauyin yanayi na shekarar 2015.

Dangane da lamarin, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Qin Gang ya bayyana a yayin taron manema labaran da aka saba yi a nan birnin Beijing a yau cewa, kasar Sin za ta ci gaba da yin hadin gwiwa da bangarorin da abin ya shafa bisa ka'idojin daukar nauyi tare amma ba iri daya ba, nuna adalci da kuma gudanar da ayyukan da abin ya shafa bisa karfinsu yadda ya kamata, domin ciyar da shawarwarin sauyin yanayi na kasa da kasa gaba, da kuma kulla wata sabuwar yarjejeniya, domin kafa wani tsarin kiyaye yanayin duniya dake dacewa da moriyar kasashen duniya cikin hadin gwiwa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China