Madam Hua ta ce, za a shirya taro karo na 20 na bangarori wadanda suka sa hannu kan "takardar dake kunshe da ka'idojin magance matsalar sauyin yanayi ta M.D.D." a birnin Lima na kasar Peru daga ran 1 zuwa ran 12 ga watan da muke ciki. Bangaren Sin yana fatan ya hadu da sauran sassa daban daban cikin halin yakini mai dacewa, kuma yana fatan za a shirya taron ba tare da wata rufa-rufa ba, bangarori daban daban za su halaci taron, tare da samun goyon bayan bangarorin da suka sanya hannu kan "takardar dake kunshe da ka'idojin magance matsalar sauyin yanayin duniya", kana za a martaba ka'idar "sauke nauyi tare amma bisa bambanci da ke kasancewa a tsakani" cikin lumana bisa karfin kowane bangare a yayin taron, ta yadda za a iya samun sakamakon da ake bukata.
Hua Chunying ta kara da cewa, a hakika dai, bangaren Sin yana ganin cewa, a yayin taron Lima, ya kamata a samu hakikanin sakamako a fannonin tabbatar da abubuwan dake kunshe cikin yarjejeniyar da za a kulla a nan gaba, da hakikanin bayanai game da yawan gudummawar da ya kamata kowane bangare ya bayar, da kuma matakan da za a dauka kafin shekara ta 2020. (Sanusi Chen)