A cikin jawabinsa a gun bikin kaddamar da taron, Ban Ki-moon ya bayyana cewa, taron Lima muhimmin taro ne kafin kasashen duniya su yi shawarwari a matakin karshe a taron Paris da za a gudanar a badi. Wakilai daga bangarori daban daban ne ke halartar taron don cimma yarjejeniyar tinkarar sauyin yanayi, a kokarin da suke na kiyaye yawan karuwar zafin yanayi a duniya da kasa da digiri 2 na ma'aunin Celcius.
Ban da wannan kuma, Ban Ki-moon ya nuna yabo ga kasar Sin, da Amurka, da kungiyar EU kan sanarwar da suka gabatar game da tinkarar sauyin yanayi, ya ce, wannan zai taimaka wajen cimma yarjejeniyar tinkarar sauyin yanayi ta duniya a shekarar 2015. (Zainab)