in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi kira da a dunkule domin tunkarar matsalar sauyin yanayi
2014-12-11 10:58:58 cri

Babban sakataren MDD Ban Ki-moon, ya bukaci shugabannin kasashen duniya da su tashi haikan domin jagorantar yaki da matsalar dumamar yanayi na duniya.

A yayin da yake jawabi ga taron shugabannin kasashen duniya karo na 20, a kan yarjejeniyar sauyin yanayi da yanzu haka ake gudanarwa, Ban Ki-moon ya ce, dole ne gwamnatoci su hada kai da kamfanoni, da hukumomi na kudi da kungiyoyin kare hakkin bil'adama da malaman jami'o'i da kuma dukkanin bangarorin ci gaba, domin daukan matakai na tunkarar sauyin yanayi.

Ban Ki-moon ya ce, yin aiki kafada da kafada da juna zai taimaka wajen kawar da matsaloli na talauci, tare da bunkasa tattalin arzikin kasashe da kuma kawo kariya ga bil'adama da duniya baki daya.

Babban sakataren MDD ya yi na'am da alkawurran da kasashen duniya suka cika na ba da gudumuwa ga asusun samar da ingantaccen yanayi.

Ban Ki-moon ya ce, kawo ya zuwa yanzu asusun ya tara jimlar kudi har dala biliyan 10, daga nan sai ya gabatar da kira ga kasashen da ba su bayar da tasu gudumuwar ba, da su hanzarta ba da tasu gudumuwar domin taimaka wajen daukar nauyin inganta yanayin da duniya take ciki. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China