in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar G77 da kasar Sin sun yi kira da a cimma sabuwar yarjejeniyar tinkarar sauyin yanayi
2014-12-10 15:27:57 cri
A jiya Talata ne aka kaddamar da taron koli na MDD kan batun sauyin yanayi a birnin Lima, shugaban kasar Bolivia Evo Morales da ke wakiltar kungiyar G77 da kasar Sin ya yi kira da a cimma sabuwar yarjejeniyar tinkarar sauyin yanayi dake maida hankali kan moriyar jama'ar kasashe masu tasowa da farko.

Morales ya yi nuni da cewa, akwai bukatar kasashen duniya su yi kokari tare wajen tinkarar sauyin yanayi, sannan kamata ya yi kasashe masu ci gaban masana'antu su cika alkawarinsu, da hanzarta baiwa kasashe masu tasowa tallafi kudi da fasahohi ta yadda za su tinkari matsalar sauyin yanayi, tare da cimma yarjejeniyar tinkarar sauyin yanayi, wato wata dokar tinkarar sauyin yanayi, a gun taron MDD kan batun sauyin yanayi da za a gudanar a birnin Paris a shekarar 2015. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China