Magatakardar MDD Ban Ki-moon ya jinjina game da sakamakon babban tarom sauyin yanayi da aka yi a birnin Lima na kasar Peru, yana mai yaba wa mahalarta taron game da yadda suka tsara jadawalin da za'a tattauna a shekara mai kamawa.
Ban Ki-moon ta bakin kakakinsa ya ce, batutuwan da aka cimma a Lima da suka hada da kiran Lima a kan sauyin yanayi, sun samar da hanya da za'a bi a amince da yarjejeniya mai ma'ana a duniya baki daya a shekara ta 2015.
Mr. Ban Ki-moon ya bukaci dukkan bangarori a taronsu na farko a watan Fabrairu na shekara mai zuwa da su yi tataunawa mai ma'ana a kan aikin tsara kashin farko na yarjejeniyar shekara ta 2015 da za ta fito sakamakon babban taron.
Daga nan sai ya jinjina wa mahalarta taron saboda yunkurin ci gaba da suka yi mai muhimmanci wajen bayyana bukatunsu da za'a shirya tare da gabatarwa a karkashin shirin kasa na ba da gudunmuwa wato INDC ga sabuwar yarjejeniya wajen tabbatar da gyara ta karshe a shirye shiryen da ake yi. (Fatimah)