Bayan kara lokacin yin shawarwari na fiye da sa'o'i talatin har zuwa safiyar ranar Lahadi, daga karshe bangarorin sun cimma ra'ayi guda domin fitar da wata yarjejeniyar dake dogaro kan wani tsarin matakin da aka taba ma gyara sau da dama.
A tsawon makwani biyu na baya bayan nan, wakilai daga kasashe fiye da 190 da kungiyoyi sun halarci taron Lima domin tattauna wata sabuwar yarjejeniyar yaki da sauyin yanayi, da ya kamata a amince da ita a karshen shekarar 2015 a birnin Paris kuma ta fara aiki a shekarar 2020. (Maman Ada)