in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yaba kasar Sin kan yadda ta jagoranci matsalar tinkarar sauyin yanayi
2014-12-11 14:44:00 cri
A jiya ne babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya gana da shugaban tawagar kasar Sin a taron sauyin yanayi na birnin Lima kana mataimakin shugaban kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin Xie Zhenhua inda ya nuna yabo ga kasar Sin kan yadda ta jagoranci aikin tinkarar sauyin yanayi.

Ban Ki-moon ya bayyana cewa, hadaddiyar sanarwar da Sin da Amurka suka gabatar kan sauyin yanayi tana da babbar ma'ana, domin za ta yi babban tasiri ga shawarwari kan sauyin yanayi da ayyukan da za a gudanar kan batun, kasashen Sin da Amurka sun zama misali wajen warware matsalar ta hanyar daukar nauyi tare bisa bambancin da ke kasancewa a tsakaninsu.

Mr Ban ya kuma ce, MDD da wasu kasashe masu tasowa sun nuna yabo ga kasar Sin kan yadda ta kafa asusun hadin gwiwar tsakanin kasashe masu tasowa, da bada kyautar kudi ga MDD don yin hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa kan yadda za a tinkari sauyin yanayi.

Don haka shi da MDD suna fatan kasar Sin za ta ci gaba da jagorantar shawarwarin da za a yi kan batun sauyin yanayi, da sa kaimi wajen ganin an cimma yarjejeniya game da batun a shekarar 2015 kamar yadda aka tsara.

A nasa bangare, Xie Zhenhua ya bayyana cewa, bayan da kasashen Sin da Amurka suka bayar da hadaddiyar sanarwa kan yadda za su magance sauyin yanayi, bangarori daban daban suka nuna amincewarsu. Kasar Sin za ta yi kokarin cika alkawarin bayar da gudummawar da kasa da kasa suka yi wajen tinkarar sauyin yanayi bayan shekarar 2020 a watanni 3 na farkon shekarar badi. Kana kasar Sin za ta ci gaba da neman hanyar kara yin hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa, da dora muhimmanci kan warware matsalolin da kasashe masu tasowa suke fuskanta sosai. Mr Xie ya jaddada cewa, akwai bukatar bangarori daban daban su yi kokari tare da yin hadin gwiwa don tinkarar matsalar sauyin yanayi. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China