in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Doke Chelsea Laifin Mourinho ne
2014-12-10 16:12:42 cri

Tashar ESPN ita ma ta soki fasahar da Mourinho yake amfani da ita, inda ta ce fasahar zamani ta kwallon kafa ta sa ana mai da hankali kan canza 'yan wasa, domin kowa ya samu damar hutawa, sabanin yadda Chelsea ke bin na ta tsarin, matakin da ya zama mai ban mamaki.

Ana iya cewa sakamakon taurin kai da Mourinho ke nunawa, wasu 'yan wasan sa su kan galabaita, yayin da wasu ke zaune a gefe suna hutawa.

Wannan mataki da Mourinho ya dauka na dada raunana karfin kungiyar ta Chelsea. Sau da yawa a farkon kakar wasa, 'yan wasan kungiyar da ke cikin yanayi mai kyau, su kan samu damar lashe sauran kungiyoyi cikin sauki. Amma sannu a hankali, bisa yadda suke kara buga wasanni 2 ko 3 a mako guda, wasu fitattu daga cikin su na fara nuna alamar gajiya, yayin da sauran 'yan wasan dake jiran canji su ma ba sa cikin yanayi mai kyau, sakamakon dadewa ba su buga wasanni ba.

Idan mun dubi tarihin Mourinho, za mu iya ganin dagewarsa kan manufar rashin gudanar da canji na 'yan wasa, lamarin da ya sanya dukkan kuloflikan da ya jagoranta, kamar Inter Milan, Chelsea, da Real Madrid, sun kan fi samun nasara a farkon wasannin su. Amma bayan hutun rabin lokaci, sai a ga karfin 'yan wasan na raguwa sannu a hankali.

Ban da wannan, akwai wata karin matsala da kungiyoyin da Mourinho ke horaswa ke gamuwa da ita. Wato batun samun raunuka, wato da yawa daga 'yan wasan kungiyoyin da yake jagoranta na fara samun rauni cikin shekara ta 3 da kasancewa tare da kocin.

Ga misali, yayin da Mourinho yake jagorantar Chelsea a shekarar 2004 zuwa ta 2007, ba a samu 'yan wasan da suka ji rauni sosai ba a shekaru 2 na farko, sai zuwa kakar wasa ta 2006 zuwa ta 2007, inda 'yan wasa da yawa suka gamu da wannan matsala. A lokacin, Didier Drogba, Frank Lampard, dan wasan baya Ricardo Carvalho, da dan wasan tsakiya Michael Ballack, dukkansu sun ji raunuka. Matsalar da ta janyo matukar raunanar karfin kungiyar. Kuma idan mun yi la'akari da yadda Mourinho ke son yin amfani da 'yan wasa kalilan, za mu ga cewa tilas ne wannan matsala ta abku.(Bello Wang)


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China