in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Doke Chelsea Laifin Mourinho ne
2014-12-10 16:12:42 cri

Yau za mu mai da hankali kan shahararren kulob din wasan kwallon kafar Birtaniya ne wato Chelsea, wanda ya rasa nasarar wasan sa da Newcastle, wasan da aka tashi Newcastle na da 2 Chelsea na da 1.

Wasan na ranar Asabar dai ya kasance karo na farko da Chelsea ya rasa nasara a wannan kaka ta bana.

Mun dai san Chelsea kungiya ce mai karfi sosai, wadda ke kunshe da kwararrun 'yan wasa da yawa, amma rashin nasarar ta a wannan karo ba ya rasa nasaba da kuskuren babban kocin ta Mourinho, musamman a fannin jagorancin fitattun 'yan wasansa.

Kafin wannan wasa Chelsea ta lashe Tottenham Hotspur da ci 3 da nema a ranar Alhamis da ta gabata. Sai dai bayan wannan wasa 'yan wasan na Chelsea ba su samu damar hutawa ba, maimakon haka, nan take suka tashi zuwa birnin Newcastle domin taka wasan ranar Asabar. Wanda hakan ke nuna 'yan wasan kungiyar suna cikin yanayi na matukar gajiya.

Ya yin wasan na Chelsea da Newcastle, za a iya ganin yadda 'yan wasan kungiyar suka nuna gajiyawa ainun. Ga misali, Francesc Fabregas, wanda ya buga wasanni 15 a jere, bisa matsayin daya daga cikin manyan 'yan wasan dake matakin farko, ya kasa nuna kwarewarsa a wannan karo, ganin yadda cikin kwallaye 105 da ya sanyawa abokan kwallon sa, kusan 24 ba su kai gare su ba, duk da cewa ya shahara ne a dalilin yadda yake iya mika kyakkyawar kwallo, musamman ma wajen mika kwallo nesa.

A nasa bangaren, Eden Hazard, wanda ya yi fice wajen gudu, a wannan wasa ya yi kokarin wuce wasu 'yan wasa 11, sai dai a karshe ya samu damar wuce 4 daga cikinsu ne kawai.

Matsala ita ce duk lokacin da Hazard ya nemi wucewa wani ba tare da samun nasara ba, to, nan take Newcastle ke samun damar kai na su harin. Ta wannan fasaha Newcastle ya jefawa Chelsea kwallo ta 2. A lokacin da Hazard ya kutsa kai bangaren Newcastle shi kadai, yayin da Kerr Barker ya kwaci kwallo daga wajensa, nan da nan shi da wasu 'yan wasan 2 suka hari gidan Chelsea, suka kuma samu damar cin wannan kwallo.

Sa'an nan mai tsaron bayan Chelsea Gary Cahill shi ma, ma iya cewa ya nuna gazawa, ganin yadda ya kasa tare kwallon da Shola Ameobi ya taho da ita kusa da ragar Chelsea, kwallon da ta ratsa tsakiyar kafafuwansa, kana dan wasan Senegal Papiss Cisse ya dauke ta ya kuma jefa a zare.

Haka kuma game da kwallo ta 2 da Newcastle ta ci, yayin da Kerr Barker ya mika kwallo, Gary Cahill ya san Moussa Sissoko ne zai dauka, sai dai bai iya kama Sissokon ba duk da kokarin da ya yi na bin sa a guje.

Sauran 'yan wasan Chelsea kuwa ma iya cewa taurarinsu sun dissashe a wannan karo. Ga misali, dukkan kwallayen 2 da aka zura musu, sun shigo ne ta bangaren dama, inda Branislav Ivanovic yake tsaro, amma ya kasa bada kariya wadda ake da bukata.

A nashi bangaren, Oscar Emboaba Junior, shi ma bai nuna wata kwarewa sosai ba, ganin yadda dukkan kwallaye 2 da ya buga suka kauracewa ragar Newcastle.

Yayin da ake buga wasa, a kan gano canzawar yanayin 'yan wasa, a wani lokacin taurarin 'yan wasan na haskakawa, yayin da a wani sa'in su kan gaza nuna kwarewa. Sai dai don magance wannan matsala, matakin da masu horas da 'yan wasan kan dauka ya kan hada da canza 'yan wasan a kai a kai, domin dukkansu su samu damar hutawa. Amma Mourinho duk da kasancewar sa kwararren koci ba ya son canza 'yan wasansa.

Yanzu dai an riga an buga zagayen wasanni har 15 a gasar Premier, sai dai har ya zuwa yanzu 'yan wasan Chelsea da suka buga wasanni a matakin farko ba su wuce 17 ba, jimilla mafi kankanta bayan ta kulaf din Southampton dake da 'yan wasa 15.

Yayin da sauran manyan kuloflika, ga misali Man. City ke da 'yan wasa 20 a rukunin farko, sa'an nan Man. United ke da 24. Shi Arsenal 'yan wasan sa dake wannan rukuni 21 kacal, yayin da Liverpool ke da 22.

Alakar wannan batu da waccan rashin nasara da Chelsea ta samu shi ne, bisa tsari canza 'yan wasa da dama na taimakawa wajen cimma nasarar wasanni, sai dai hanyar da Mourinho yake bi ta tsayawa kan 'yan wasa rukunin sa na farko ta kan sanya 'yan wasansa gajiya matuka.

Yanzu haka dai 6 daga cikin 'yan wasan Chelsea sun buga dukkan wasanni zagaye 15, jimillar da ta dara ta sauran kulaflikan dake buga gasar Premier.

Jaridar Daily Post ta kasar Birtaniya ta taba bayyana cewa, idan mutum ya rufe idanunsa nan take zai iya lasafta 'yan wasan da Mourinho zai yi amfani da su a matakin farko. Jerin sunayen ya kan kunshi mai tsaron gida Thibaut Courtois, da 'yan wasan baya Branislav Ivanovic, Gary Cahill, John Terry, César Tanco. Sai 'yan wasan tsakiya Fabregas Soler, da Nemanja Matic, William da Silva, Oscar, Eden Hazard, da Diego Costa, muddin dai cikinsu ba wanda ya ji rauni, ko kuma aka hana shi halartar wasa.

Sai dai masu nazarin kwallon kafa da dama na ganin wannan al'ada ta Mourinho na ba 'yan wasansa wahala, ganin bisa kididdiga Fabregas ya yi gudun da ya kai kilomita 164 a wasannin zagaye 14 da ya halarta, wato kimanin kilomita 12 a ko wane wasan da ya buga ke nan. Yayin da a nasa bangaren, Matic nisan gudun da ya yi, ya kai kilomita 143 a wasanni karo 14 da ya fara bugawa. Ban da wadannan, Fabregas dake taka leda a tsakiyar filin wasa, matsayinsa na bukatar ya kai hari gaban gidan abokan karawa, gami da komawa baya domin taimakawa 'yan baya, ayyukan da ake bukatar ya yi su cikin sauri, don haka ya kan fi sauran 'yan wasa gajiya.

Sai dai idan mun dubi tarihin Mourinho, za mu ga cewa da ma al'adarsa ce rashin son canza 'yan wasa. Dalilin da ya sa haka kuwa shi ne; Babban kocin yana dora muhimmanci kwarai ga tsaron gida, saboda haka yake da bukatar tsarin tsaron baya mai karko. Idan kuwa aka cire wani dan wasa daga wannan tsarin tsaron gida, hakan na iya karya dukkanin tsarin.

Kamar yadda a wannan karo Newcastle ya ci Chelsea 2 da 1, kusan dukkan kafofin watsa labaru na kasar Birtaniya na ganin cewa, hakan na da nasaba da rashin Matic a wasan, ganin cewa ragowar 'yan wasan ba su iya taka rawar da Matic ke takawa a fannin tsaron gida.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China