in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Doke Chelsea Laifin Mourinho ne
2014-12-10 16:12:42 cri

Matic wanda ya ke da gudu, da iya sarrafa kwallon sama, kuma ya iya mika kwallon duk wurin da yake so, gami da lura da matsayinsa a filin wasa. Wadannan fasahohi na sa, sun sa ya zama ginshiki a kungiyar Chelsea a fannin tsaron gida. A nasa bangare, Mourinho ya san Mikel John Obi ba zai iya maye gurbin Matic ba. Saboda haka, ya bukaci Mikel ya yi kokarin dakile kwallayen da zasu biyo ta wurin sa, manufar da ta hana Mikel din nuna kwarewarsa. Saboda haka, duk da cewa Mikel shi ma shahararren dan wasa ne mai fasaha, amma ya gaza baiwa kulaf din na sa gudummowar da ta dace, hakan kuwa ya sa an samu raguwar kai hari cikin sauri daga bangaren kungiyar ta Chelsea.

Hakika dai Fabregas da Matic sun kasance ginshikai 2 a kungiyar Chelsea, domin duk lokacin da su biyun suka shiga wasa tare, kungiyar na nuna karfin ta a bayyane, wajen kai hari da tsaron gida. Amma idan daya daga cikinsu ba ya cikin wasan, kungiyar kan gamu da matsala.

Da ma Mourinho kan ce Chelsea ba wata kungiyar ce da ta gagara ba. Yana kuwa fadin hakan ne domin ya san wasu 'yan wasan kungiyar suna da muhimmanci kwarai. Ta yadda idan ba sa cikin kungiyar, Chelsea ba ta iya nuna cikakken karfinta. Kuma dalilin da ya haifar da wannan yanayin da kungiyar take ciki kuwa shi ne, kasancewar Mourinho ya fi dogaro kan 'yan wasan da ya kan yi amfani da su a matakin farko, yayin da sauran 'yan wasan sa masu jira ba sa samun isasshen lokacin buga wasa, lamarin da ya sanya kullum din gaza kasancewa cikin yanayi mai kyau.

Misali a nan shi ne dan wasan kasar Jamus Andre Schurrle, wanda ya halarci kungiyar Chelsea a kakar wasar 2013 zuwa 2014. Tsakanin wannan lokaci ya buga wasanni 30, inda a wasanni 15 ya kasance cikin 'yan wasan dake a matakin farko, yayin da a sauran wasanni 15 yake jira.

Har ya zuwa yanzu ana iya tunawa da yadda ya ci kwallonsa ta farko, a wasan da Chelsea ta lashe Man. City 2 da 1. Kuma ganin yadda ya nuna kwarewarsa a lokacin, ya sa aka zaci zai samu karin damar taka leda a wannan kakar wasa. Amma maimakon haka ya kasance cikin 'yan jiran canji, bayan wasanni 3 na farko da ya buga. Duk kuwa da cewa dan wasan ya bada gudunmowa sosai ga kungiyar kasar Jamus, ya yin da ta lashe gasar cin kofin duniya da ta gabata a Brazil.

A nasa bangare, Filipe Kasmirski, shi ma bai samu damar nuna kwarewarsa ba. A wannan kakar wasa, ya halarci wasanni 6 ne kawai, gaba daya ya buga wasa na tsahon mintuna 263 ne kawai. Idan ba a manta ba, kafin ya sauya sheka zuwa Chelsea, ya kasance dan wasa mai muhimmanci a kulaf din Atletico Madrid. Amma duk da haka, Mourinho bai ba wannan dan wasa na kasar Brazil dama sosai ba.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China