in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zakarar gudun yada kanin wani ta bayyana aniyar kare kambin ta a Beijing
2014-12-05 10:00:25 cri
Zakarar gudun yada kanen wani ta duniya daga kasar Kenya Edna Kiplagat, ta bayyana aniyar kare kambin ta, a gasar tsere ta shekarar 2015 dake tafe a nan birnin Beijing.

Kiplagat, 'yar shekaru 35, ta ce tana da burin kafa tarihi, na kasancewa mace ta farko da ta lashe lambar tseren duniya har karo 3, bayan da ta samu nasara karo 2 a baya.

'Yar tseren dai ta lashe gasar duniya ta farko ne a shekarar 2011 a birnin Daegu na Koriya ta Kudu, ta kuma sake lashe wannan gasa a birnin Moscow a shekarar 2013.

Kiplagat, wadda ta zanta da manema labaru a ranar Asabar, ya yin bikin bude wani sabon filin tsere da aka gina, a filin wasan makarantar "Gems Cambridge International" dake birnin Nairobi, ta kara da cewa ta na fatan ci gaba da samun nasarori a kakar wasanni dake tafe, koda yake kare kambin ta shi ne buri mafi muhimmanci a gare ta.

Kaza lika ta alkawarta baiwa marada-kunya, a gasar tsere ta birnin London dake tafe, matakin da zai ba ta damar kasancewa cikin tawagar kasar ta Kenya a gasar duniya.

A daya bangaren kuma, bikin bude filin wasan tseren ya samu halartar karin shahararrun 'yan tsere, ciki hadda zakaran gudun mita 1500 ajin maza Asbel Kiprop, wanda ya yin zantawar sa da mane ma labaru shi ma ke cewa shima yana fatan kare kambin sa a watan Agustan dake tafe.

Kiprop, wanda ya bayyana damuwa ga karuwar 'yan wasa masu ta'ammali da kwayoyi, ya ce akwai bukatar daukar karin matakan dakile wannan laifi. A cewar sa kara tsawon takunkumin da ake sanyawa 'yan wasan da suka karya dokokin wasa na iya sanya 'yan wasan kauracewa wannan mummunar al'ada.

A baya bayan nan dai ana samun karuwar zargin 'yan wasa masu ta'ammali da kwayoyi, ciki hadda Rita Jeptoo, daya daga manyan 'yan tseren kasar ta Kenya, wanda samun sa da lafin shan kwayoyi ya haifar da damuwa matuka a fannin harkar wasannin motsa jiki.

Kiprop na ganin idan har aka dada tsahon lokacin da ake dakatar da 'yan tsere shiga gasanni idan har aka same su da amfani da kwayoyi, hakan zai sanya kowa shiga taitayin sa, a kuma samu raguwar wannan laifi.

Kasar Kenya dai na cikin kasashen nahiyar Afirka dake da hazikan 'yan tsere, da suka sha samun nasarori a gasannin tsere na duniya da ake shiryawa.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China