Rahotanni dai sun ce Phillip Hughes ya rasu ne kwanaki biyu, bayan da kwallo ta kwace ta same shi, ya yin wasan da ya buga da wata kungiyar kudancin Australia a ranar Talatar makon na jiya.
Yanzu haka dai an dage wasan da a baya aka tsara gudanarwa a ranar Alhamis, a kuma gabar da aka shirin gudanar da bikin binne gawar Hughes a garin Macksville dake New South Wales a Laraba 3 ga watannan Disamba.
Da yake tsokaci game da wannan batu shugaban hukumar wasan Cricket na kasar Australia James Sutherland, ya ce 'yan wasan kasar na cikin halin jimami, don haka mawuyaci ne su iya buga wasa a irin wannan hali.
"Muna godiya ga irin fahimta da hukumar Cricket ta India ta nuna don gane da wannan mawuyacin hali da muke ciki", a kalaman Sutherland.(Saminu Alhassan)