A wannan rana, Xie Zhenhua ya halarci taron kara wa juna sani kan tunkarar matsalar sauyin yanayi, inda ya bayyana sakamakon da kasar Sin ta samu cikin 'yan shekarun nan wajen fuskantar sauyin yanayi, ya ce, kasar Sin tana dukufa kan fuskantar sauyin yanayi da kuma kiyaye muhalli, yayin da take kokarin bunkasa tattalin arzikinta da kuma kyautata zaman rayuwar al'ummomin kasar yadda ya kamata.
Haka kuma, tun shekarar 2014 ne, kasar Sin ta fara aiwatar da "shirin fuskantar sauyin yanayi daga shekarar 2014 zuwa 2020", sa'an nan ta sanar da burin da ta ke son cimmawa bayan shekarar 2020 a wannan aikin.
Bugu da kari, ya ce, tun daga shekarar 2011 kasar Sin take inganta hadin gwiwar kasashe masu tasowa ta fuskar sauyin yanayi cikin himma da kwazo, gaba daya kasar Sin ta samar da dallar Amurka miliyan 44 wajen ciyar da hadin gwiwar kasashe masu tasowa kan wannan aiki, ta kuma kafa asusun magance matsalar sauyin yanayi na kasashe masu tasowa.
Ya kuma kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da taimaka wa kasashen da abin ya shafa bisa bukatunsu kan wannan aiki. (Maryam)