Su Wei ya bayyana cewa, taron Lima yana da muhimmanci ga cimma wata sabuwar yarjejeniya kan tinkarar sauyin yanayi bayan shekarar 2020 a birnin Paris, kuma warware matsalolin dake kunshi cikin yarjejeniyar da kuma yadda za a tattara kudi su ne muhimman batutuwan da za a tattauna a taron Lima.
Game da hadaddiyar sanarwa kan sauyin yanayi a tsakanin Sin da Amurka kuwa, Su Wei ya bayyana cewa, ma'anar sanarwar shi ne shugabannin kasashen biyu suna iya fuskantar hasarar da aikin rage abubuwa masu gurbata muhalli zai kawo a fannonin bunkasuwar tattalin arziki da samun wadata a kasashen biyu. Kana sanarwar wata hanya ce da kasashen biyu suka sa kaimi don a samu ci gaba kan shawarwarin sauyin yanayi na duniya. Haka kuma sanarwar ita ce hadaddiyar sanarwar da aka nuna girmamawa da juna, wadda ta iya taimakawa da samun sakamako a shawarwarin sauyin yanayi.
Su Wei yana fatan ita kasar Japan za ta taka muhimmiyar rawa a sabuwar yarjejeniyar da za a cimma a birnin Paris a shekarar 2015, da kuma gabatar da sabon burinta na rage abubuwa masu gurbata muhalli bayan shekarar 2020.
Ban da wannan kuma, Su Wei ya bayyana cewa, kasar Sin tana yin bincike kan shirin game da gudummawar da kasa da kasa suke son bayar wajen tinkarar sauyin yanayi, kuma watakila za a gabatar da shi kafin farkon rabin shekarar badi. (Zainab)