Babbar wakiliyar yin shawarwari ta kwamitin kungiyar EU Elina Bardram ta bayyana cewa, taron Lima zai zama muhimmin taro kafin taron Paris, don haka kungiyar EU tana fatan za a samu sakamako mai amfani a taron Lima.
Elina ta bayyana cewa, ana bukatar a warware matsaloli da dama a cikin makwanni biyu masu zuwa, sai dai kuma halin tinkarar sauyin yanayi da ake ciki a duniya ya kyautata. Ta ce, kungiyar EU ta zartas da wasu yarjejeniyoyin tsarin yanayi da makamashi na shekarar 2030 a watan Oktoba na bana, haka kuma kasashen Sin da Amurka sun gabatar da hadaddiyar sanarwar tinkarar sauyin yanayi a watan Nuwanba, matakan da suka nuna alama ga sauran kasashen duniya, wadanda za su sa kaimi gare su da gabatar da shirye-shiryensu a wannan fanni kafin taron Paris. (Zainab)