Kana Yu Zhengsheng ya bayyana cewa, inganta hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashen Afirka muhimmin tushe ne na manufofin harkokin wajen kasar Sin. Har ila yau Sin tana burin kara yin mu'amala tare da bangarori daban daban, da kara yin hadin gwiwa a tsakaninta da kasashen Afirka, da kuma sa kaimi ga samun zaman lafiya da bunkasuwa a nahiyar Afirka.
A nasa bangare, Nujoma godiya ya yi ga kasar Sin domin gudummawar da take bayarwa wajen sa kaimi ga samun bunkasuwa a Afirka. Kana ya bayyana cewa, kasarsa ta dora muhimmanci kan raya dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin, kuma tana son kara yin hadin gwiwa a fannonin siyasa, da tattalin arziki, da cinikayya, da al'adu da dai sauransu. Bugu da kari, kasarsa tana burin koyon fasahohin Sin a fannin bunkasa tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar jama'a, da kuma kara sada zumunta a tsakaninta da kasar Sin. (Zainab)