Wakilin din-din-din na kasar Sin a MDD Wang Min, ya yi kira ga al'umomin kasa da kasa da su dauki matakan da suka wajaba na kara kare lafiyar ma'aikatan da ke aikin jin kai.
Wang Min wanda ya yi wannan kiran yayin taron kwamitin sulhu na MDD game da kare lafiyar ma'aikatan da ke aikin jin kai a wuraren da ake gwabza fada da makamai, ya ce ana kaiwa ma'aikatan hare-hare na ba gaira ba dalili har ma wasu kan rasa rayukansu sakamakon wadannan hare-hare.
Manzon na Sin ya yi allah wadai da irin wadannan hare-hare da ake kaiwa ma'aikatan jin kai, yana mai cewa, hakkin dukkan bangarorin da ke gwabza fada ne su kare rayukan ma'aikatan jin kan. Don haka ya ce, akwai bukatar MDD, kasashe mambobin MDD da hukumomin bayar da agaji su dauki matakan da suka dace wajen ganin an kare lafiyar ma'aikatan.
An kebe ranar 19 ga watan Agustan kowa ce shekara ce a matsayin ranar ayyukan jin kai ta duniya da nufin karrama kokarin da ma'aikatan jin kan ke gudanarwa. (Ibrahim)