in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'an MDD sun bukaci da a goyi bayan ayyukan jin kai a duniya baki daya
2014-08-20 10:40:02 cri
A ranar Talata 19 ga wata ne manyan jami'an MDD suka karrama ma'aikatan jin kai da suka gudanar da ayyukan ceton rai a sassan duniya daban-daban tare da yin kiran da a goyi bayan ayyukan jin kai da ake gudanar wa a duniya baki daya.

Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya ce, hare-haren da ake kaiwa ma'aikatan jin kai, yana hana jama'ar da ke bukatar samun taimakon jin kai da suke bukata.

Bayanai sun nuna cewa, a shekarar 2013 kadai, an kashe ma'aikatan jin kai 155, yayin da 171 suka ji mummunan rauni kana aka sace 134, adadin da ya nuna karuwar kashi 66 cikin 100 na ma'aikatan jin kai da suka tagayyara idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

Wasu alkaluma sun kuma nuna cewa, ya zuwa ranar 15 ga watan Agusta, an kashe ma'aikatan jin kai 79 a wannan shekara kadai, inda a watannin Yuli da Agusta aka samu karuwar hare-hare kan ma'aikatan jin kai ciki har da Gaza da Sudan ta Kudu.

Shugaban babban zauren MDD John Ashe ya ce, ranar ba wai wata dama ce ga al'ummomin kasa da kasa na yin biki don muhimmancin wannan aiki ba, amma wata dama ce ta nazari don kara daura damara, yayin da miliyoyin jama'a ke bukatar taimakon jin kai sakamakon yaki da sauran bala'u daga indallahi.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China