Ofishin hukumar kula da ayyukan jin kai na MDD OCHA, ya bayyana matukar damuwarsa, don gane da matsalolin da ake fuskanta, game da shigar da kayan agajin jin kai yankunan dake tsakiya, da kuma gabashin kasar Somaliya.
Wata sanarwa da OCHAn ta fitar a jiya Alhamis, ta ce, dauki ba dadin da sojojin gwamnati da na kungiyar AU ke yi da dakarun kungiyar Al-Shabaab ya tsananta a wannan wata. Matakin da ke kawo cikas ga burin da ake da shi, na sada dubban jama'ar wadannan yankuna da agajin jin kai.
Duk dai da yanayin da ake ciki, OCHA na burin matakin sojin da ake dauka yanzu haka, zai kawo karshen rigingimu, tare da ba da damar kafa gwamnati mai nagarta, da za ta tallafi shirin agajin yadda ya kamata.
Ya zuwa yanzu dai rahotanni sun bayyana cewa, rundunar wanzar da zaman lafiya ta kungiyar AU ko AMISOM a takaice, da hadin gwiwar rundunar sojin gwamnatin Somaliya, sun kai ga yantar da yankin yammacin kasar daga ikon dakarun kungiyar Al-Shabaab. Matakin da aka bayyana da babban jigon tabbatar da tsaro, da wanzar da doka da oda. (Saminu)