in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabbin fadace-fadace a Sudan ta Kudu sun kawo cikas ga ayyukan jin kai, in ji UNICEF
2014-03-04 10:30:00 cri

Daraktan lura da shirin agajin gaggawa na asusun yara na MDD UNICEF Mr. Ted Chaiban, ya ce, sabbin fadace-fadace dake wakana a sassan kasar Sudan ta Kudu, sun haifar da babban koma baya, ga ayyukan ba da agajin jin kai da ake gudanarwa yanzu haka.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin a birnin Nairobin kasar Kenya, Mr. Chaiban ya ce, duk da rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta da aka yi cikin watan Janairun da ya gabata a kasar Habasha, dakarun gwamnati, da na 'yan tawaye na ci gaba da kaiwa juna hari, tare da zargin juna bisa tabarbarewar halin da kasar ke ciki.

A cewar waccan sanarwa, ya zuwa yanzu akwai daruruwan mata, da kananan yara da ba sa samun isasshen abinci, da tsaftacaccen ruwan sha da kuma kayan kulawa da lafiya, matakin da ka iya jefa rayuwarsu cikin hadari.

Bugu da kari, kimanin mutane 900,000 da rabin su yara kanana ne, sun tserewa daga kasar. Baya ga wasu karin mutane 30,000 da ake hasashen na iya rasa matsugunansu nan da 'dan lokaci.

Haka zalika, akwai rahotannin kisan kiyashi, fyade, da keta alfarnar bil'adama, da ake zargin sassan dakarun gwamnati da na 'yan adawa sun aikata a kasa. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China