Sakatariyar MDD mai lura da ayyukan jin kai Valerie Amos, ta bayyana tashe-tashen hankula da yake-yake, a matsayin dalilan dake haifar da koma baya ga ayyukan jin kai a sassan duniya daban daban.
Amos wadda ta bayyana hakan yayin zantawarta da wakilin kamfanin dillancin labarun kasar Sin Xinhua, ta ce, hukumarta na fuskantar tarin kalubale, a kasashen da suka dade suna fama da tashe-tashen hankula kamar jamhuriyar dimokaradiyyar Congo, da Afirka ta Tsakiya, da Somaliya da Yemen.
Ta ce, irin wannan hali na matsi ya tilastawa dubban al'ummun kasashe a Afirka ta Tsakiya da Mali kauracewa gidajensu, matakin da a cewarta ya taka muhimmiyar rawa wajen dakile ci gaban yankin baki daya.
Amos ta kara da cewa, irin wannan hali rikici ne da al'ummun kasashen Sham ke fuskanta, wanda kuma ke haifar da matsi da kwararar dubban 'yan gudun hijira ga makwaftanta kamar Lebanon da Jordan da kuma Turkiyya.
A daya bangaren sakatariyar MDDr mai lura da ayyukan jin kai ta bayyana bullar cutar Ebola a wasu kasashen dake yammacin Afirka, a matsayin musabbabin bukatuwa ga karin ayyukan jin kai daga MDD. Wannan annoba, a cewarta, ta haifar da koma baya ga aniyar da ake da ita na samun ci gaba a kasashen da cutar ta bulla.
Daga nan sai ta bayyana aniyar hukumarta, da ma daukacin masu ruwa da tsaki, wajen tattara kudade, da tallafin da ya dace, domin agazawa al'ummun da ke cikin mawuyacin hali, baya ga kokarin da ake yi na bunkasa hadin gwiwa da sauran kungiyoyin ba da agaji, duka dai da nufin cimma burin da aka sanya gaba. (Saminu)