in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta ware dala miliyan 75 domin aikin jin kai a yankin Sahel da kusurwar Afrika
2014-07-24 10:07:12 cri

Mataimakiyar sakatare janar na MDD kan harkokin jin kai, Valerie Amos ta sanar a ranar Laraba cewa, an ware dalar Amurka miliyan 75 daga babban asusun kula da harkokin jin kai na MDD (CERF) domin tallafawa ayyukan jin kai a yankin Sahel da kusurwar Afrika. Ganin yadda yawan rikice-rikice suke mugun tasiri, dole hankalinmu ya karkata, domin kada a manta cewa, mutane da dama suke cikin bukata, in ji madam Amos a cikin wata sanarwa.

Kudaden za su taimaka wajen tafiyar da ayyukan jin kai a cikin kasashe goma sha daya da aka zabe su bisa dalilin halin da suke fuskanta na rashin kudi da matsaloli. Haka kuma wannan gudunmuwa za ta taimaka wajen tafiyar da ayyukan jin kai mafi muhimmanci a yankin Sahel da kusurwar Afrika, yankunan da rashin abinci mai gina jiki da karancin abinci ya fi tasiri. Kasashen ka iyar sake fadawa cikin matsaloli idan ba mu ba da taimako ba yanzu, in ji madam Amos.

Kasashen dake kusurwar Afrika za su samu dalar Amurka miliyan 44,5, kuma miliyan 20 za su je ga kasar Somaliya, inda mutane miliyan 2,9 suka rasa issashen abinci.

Cibiyoyin agaji a kasashen Habasha, Kenya da Eritoria za su samu miliyan 12, miliyan 10 da miliyan 2,5 a kowanensu. Kana kuma fiye da dalar Amurka miliyan 30 za su taimaka ga ayyukan jin kai a cikin kasashe bakwai na yankin Sahel da suka hada da Nijar, Kamaru, Senegal, Burkina-Faso, Mauritaniya, Najeriya da Gambiya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China