Mataimakiyar babban sakatare mai kula da harkokin jin kai ta MDD Valerie Amos ta bayyana cewa, ko da yake wasu al'ummomin kasa da kasa na fama da rikicin jin kai mai tsanani a halin yanzu, ba za a iya samar da taimakon jin kai ga wadannan mutane yadda ya kamata ba. Kudin da MDD ta samar, za ta taimaka wa miliyoyin mutanen da ke fama da rikice-rikice ne, ba wai warware musu dukkan bukatunsu ba.
Bisa shirin MDD, kudin da za a baiwa kasar Sudan zai kai dallar Amurka miliyan 20, yayin da kasar Yemen za ta samu dallar Amurka miliyan 14, kasar Mali za ta samu dallar Amurka miliyan 11.5, kasar Chadi za ta samu dallar Amurka miliyan 10, kasar Colombia za ta samu dallar Amurka miliyan 4.5, kasar Djibouti za ta samu dallar Amurka miliyan 4, kasar Koriya ta Arewa za ta samu dallar Amurka miliyan 6.5, kasar Haiti za ta samu dallar Amurka miliyan 6, kasar Myamar za ta samu dallar Amurka 5.5, yayin da kasar Uganda za ta samu dallar Amurka miliyan 4. (Maryam)