in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da taron internet na duniya karo na farko a birnin Wuzhen na kasar Sin
2014-11-19 14:36:43 cri

An kaddamar da taron internet na duniya karo na farko a birnin Wuzhen dake lardin Zhejiang na kasar Sin a ranar 19 ga wata da safe. Domin wannan taro, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sakon taya murna cewa, a zamanin yanzu, an samu ci gaba sosai kan fasahohin zamani musamman ma a fannin fasahohin sadarwa, inda internet ta kasance abin da ke sa kaimi ga kirkiro da samun bunkasuwa, wadda ta canja zaman rayuwar jama'a da kuma taimakawa wajen inganta zamantakewar al'umma. An mai da duniyarmu ta zama tamkar wani karamin kauye bisa yin amfani da internet, da mai da jama'ar kasashe daban daban a matsayin al'ummomin dake hadin gwiwa da juna wadanda ke da kaddara guda.

A cikin sakon, shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, bunkasuwar internet ta kawo kalubale ga ikon mulkin kasa, da tsaro, da kuma bunkasuwar kasa, ana bukatar kasa da kasa su maida kulawa kanta, da yin kokari wajen raya ta da samun moriyar juna. Kasar Sin tana kokarin raya internet don amfana wa jama'ar kasar. Haka zalika kasar Sin tana son yin kokari tare da kasa da kasa da bin ka'idojin girmama juna da yin imani da juna, da kara yin hadin gwiwa, da girmama ikon mallakar internet, da tabbatar da tsaron internet, da raya internet bisa tushen zaman lafiya da tsaro da bude kofa da kuma hadin gwiwa, da kafa tsarin kulawa da yanar gizo ta internet ta tsarin demokuradiyya da bayyana kome a fili, wanda kuma zai shafi bangarori daban daban. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China