in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manzon musamman na shugaban kasar Sin ya halarci bikin jana'izar shugaban Zambiya
2014-11-12 16:42:44 cri

Manzon musamman na shugaban kasar Sin kuma ministan gidaje da raya birane da garuruwa na kasar Sin Chen Zhenggao ya halarci bikin jana'izar marigayi shugaban kasar Zambiya Michael Chilufya Sata tare da ganawa da mukadashin shugaban kasar Guy Scott.

A madadin shugaba Xi Jinping, da gwamnatin Sin da jama'arta, Mr. Chen ya isar da sakon ta'aziyyar shugaba Xi game da rasuwar marigayi Michael Sata tare da mika sakon jaje ga Guy Scott da kuma iyalan marigayi shugaba Sata.

A jawabinsa Guy Scott ya bukaci Mr Chen da ya mika godiyarsa ga shugaba Xi da jama'ar kasar Sin. Ya ce, halartar jana'izar da manzon musamman na Sin ya yi ya nuna irin sahihin zumunci dake tsakanin jama'ar kasashen biyu. Kasar Zambiya kuma za ta ci gaba da bin manufar da shugaba Sata ya kan dauka wato kara zurfafa hadin kai da sada zumunci da kasar Sin nan gaba. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China