Micheal Sata wanda ya tashi zuwa Londan a ranar 20 ga watan da muke ciki domin duba lafiyar sa ya rasu ne da misalin karfe 11 agogon GMT a asibitin King Edward VII bayan watannin da aka yi ana ta rade rade game da lafiyar jikinsa, kamar yadda Sakataren gwamnatin kasar Roland Msiska yayi bayani.
Rashin lafiyar marigayi shugaban kasar na Zambiya dai tun a watan Yuni ya tsananta, abin da ya sa a watan jiya ma lokacin babban taron MDD ya kasa karanta jawabinsa. Dan shekaru 77 da haihuwa, Sata wanda ya zama shugaban kasar Zambiya na biyar bayan da ya lashe zaben shugaban kasar a shekarar 2011 ya gagara halartar bikin cikar kasar shekaru 50 da samun 'yancin kai a jumma'an nan da ta gabata.
An dai haifi Marigayin ne a arewacin Zambiya a ranar 6 ga watan Yuli a shekarar ta 1937 kuma yana daya daga cikin jigajigan siyasar kasar inda ya rike mukamai da dama a gwamnatocin baya tun daga zamanin Kenneth Kaunda.(Fatimah)