in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar Li Yuanchao za ta kara inganta dangantakar dake tsakanin Sin da Zambia
2014-06-19 15:08:10 cri
Jaridar Zambian Times ta bayar da wani sharhi a ranar 18 ga wata, inda ta bayyana cewa, ziyarar da mataimakin shugaban kasar Sin Li Yuanchao ya kai a kasar Zambia ta bayyana burin kasashen biyu na raya dangantakar abokantaka a tsakanin su a dukkan fannoni, kana ziyarar za ta sa kaimi ga kasashen biyu wajen samun moriyar juna.

Sharhin ya kuma musanta zargin da kafofin yada labarai na kasashen yammacin suka yi wa kasar Sin kan cewa wai tana raya dangantakar dake tsakaninta da kasashen Afirka don kwace albarkatun nahiyar Afirka. Sharhin ya nuna cewa, ayyukan bada gudummawa da zuba jari ga nahiyar Afirka da kasar Sin ta yi sun taimakawa kasashen Afirka wajen samun bunkasuwa, saidai wadannan ayyuka an yi su ba tare da sharadi ba, wannan ita ce maganar gaskiya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China